Boko Haram

Nijar ta dage haramcin karbar ‘Yan gudun hijira

'Yan gudun Hijira Diffa, a Najeriya
'Yan gudun Hijira Diffa, a Najeriya AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA

Gwamnatin Nijar ta sanar da dage haramcin karbar ‘Yan gudun hijira da ke kauracewa rikicin Boko Haram kuma wadanda ke ci gaba da kwarara a cikin kasar. Nijar ta haramta karbar ‘Yan gudun hijirar saboda tsoron Boko Haram na iya fake a sansanin domin kaddamar da hari a cikin kasar.

Talla

Daruruwan ‘Yan gudun hijira ne ke ci gaba da kwarara a Diffa da ke kan iyaka da yankin arewa maso gabacin Najeriya mai fama da hare haren Mayakan Boko Haram.

Mahukuntan Nijar sun bayyana fargaba akan yawan mutanen da ke kwarara zuwa kasar mai fama da matsalar ci-maka.

Matakin dage haramcin dai na zuwa ne bayan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta lallashi Nijar akan ta karbi ‘Yan gudun Hijirar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.