Sudan ta Kudu

Habasha na karbar bakuncin taron zaman lafiyan kasar Sudan ta Kudu

Wasu 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu
Wasu 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu Reuters

Yau Alhamis Shugaban kasar Sudan ta Kudu zai gana gaba da gaba da Jagoran ‘yan tawayen kasar, inda zasu tattauna hanyoyin da za abi don kawo karshen rikicin kasar.Ana fata tattaunawar da ake yi a kasar Ethiopia zata taimaka wajen kawo karshen yakin babasan kasar, da aka shafe watanni 13 ana gwabzawa. Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun ‘yan tawaye Riek Machar, da dakarunsu ke ci gaba da gumurzu, suna ganawar ne karkashin sa idon masu shiga tsakani daga kungiyar hadin kan kasashen gabashin Africa ta IGAD.Taron na Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha zai nemi dinke barakar da ake da ita, tsakanin bangarorin 2, don neman dawwamammen zaman lafiya a kasar ta Sudan ta Kudu.Shugabannin kungiyar ta IGAD sun ce bangarorin 2, za kuma su gana da shugannin kasashen yankin, dake shirin halartar taron kungiyar hadin kan Africa ta AU, da za a yi a birnin na Adis Ababa a ranakun Juma’a da Asabar.A farkon wannan watan na Junairu, bangarorin dake rikici da juna, suka yi ganawarsu ta karshe a kasar Tanzania, inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya karo na 6 cikin shekara daya.Yayin taron na Tanzania, dukkan bangarorin sunyi alkawarin neman afuwar ‘yan kasar Sudan ta Kudu, kan abinda ya faru tun lokacin da yaki ya barke a watan Disamban shekarar 2013.