Mali

Majalisar dunkin Duniya ta kaddamar da bincike a Mali

Le Premier ministre malien, Modibo Keïta, le 9 janvier 2015.
Le Premier ministre malien, Modibo Keïta, le 9 janvier 2015. AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE

Babban Sakataren Majalisar dunkin Duniya Ban Ki-moon ya ce yana da shirin kaddamar da binciken musabbabin mutuwar mutane uku, yayin da masu aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali suka bude wuta kan masu boren nuna kyamar Dakarunta a kasar

Talla

A ranar Talata da ta gabata ne a garin Gao na kasar Mali, aka yi zanga-zanga da ta kai ga mutuwar mutanen.

Wani mai Magana da yawun Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar ta dunkin Duniya ya ce Dakarun sun bude Wuta ne kawai da niyyar gargadi, a lokacin da masu boren ke jifansu har da bama-baman fetur da bindiga.

Dama dai kasashen Duniya na sa Ido ga kungiyoyin ‘yan tawayen Abzinawa na Mali da a shekarun baya suka dade suna kaddamar da hare-hare a kan wurare mallakar gwamnati.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.