Boko Haram

Ban ki-moon ya yi marhaba da shirin tarayyar Afirka

Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon,
Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon, REUTERS/Noor Khamis

Babban sakataren majalisar Dinkin-duniya, Ban ki-moon ya yi marhaban da shirin tarayyar Afirka a yau asabar, na kafa rundunar sojin hadin gwiwa, a Afirka ta yamma domin yakar kungiyar Boko Haram.Ban ki-moon wanda ya bayyana hakan yayyin gudanar da taron kungiyar tarayya afrika a ethopia ya ce duba ga irin ayukan da kungiyar Boko Haram suka aika ta ya kamata a kawo karshan wannan matsalar ta fuskar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka ta yamma da sauran kasashen duniya".

Talla

Kasashe biyar da suka hada da Najeriya da Kamaru da Chadi da Niger da kuma Benin su za su kafa rundunar sojin hadin gwiwar mai kushe da dakaru sojoji 7,500.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.