Zaben Najeriya: APC na zargin gwamnati da hana 'yan jaridan kasashen waje zuwa kasar

Shugaban hukumar Zaben Najeriya attahiru Jega
Shugaban hukumar Zaben Najeriya attahiru Jega Bizwatch

Babbar jam’iyar adawa ta APC a Nigeria ta zargi gwamnatin kasar da hana ‘yan jaridun kasashen waje damar gudanar da aiki a zabukan shuagabncin kasa da na yan majalisun dokokin kasar, da ake shirin yi cikin wata mai kamawa. Jam’iyyar tayi zargin cewa ana shirin yin hakan ne, ta hanyar hana wakilan da kafofin yada labaran kasashen duniya visar shiga kasar.A ranar 14 ga wata mai zuwa na Fabrairu za a yi zaben shugaban da na ‘yan majalisun dokokin kasar.