Zimbabwe

AU: Mugabe zai halarci taron kasashen yammaci

Shugaban Tarayyar Afrika Robart Mugabe na Zimbabwe
Shugaban Tarayyar Afrika Robart Mugabe na Zimbabwe REUTERS/Tiksa Negeri

Kungiyar Tarayyar Turai ta ba Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe damar halartar wasu tarukan tattaunawa saboda mukaminsa na shugaban Tarayyar Afrika duk da takun-sakar da ke tsakanin kasashen Turai da shugaban.

Talla

A makon jiya ne shugaba Mugabe mai shekaru 90 ya karbi mukamin shugaban kungiyar Tarayyar Afrika na karba-karba, matakin da ake ganin zai dagula dangantar kungiyar da kasashen yammaci.

Akwai takunkumin hana tafiye-tafiye da kungiyar Turai ta kakabawa Mugabe saboda adawa da cin zarafin mutane da keta dokokin dimokuradiya da ake zargin shugaban ya aikata a kasar Zimbabwe.

Yanzu Tarayyar Turai tace shugaban yana iya halartar taro a nahiyar Turai da ya shafi ayyukan Tarayyar Afrika.

Tun samun ‘yancin kan kasar Zimbabwe a 1980 Robert Mugabe ke shugabanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.