Burkina Faso

Sojoji sun bukaci Firaministan Burkina Faso ya yi marabus

Firaministan Burkina Faso Isaac Zida
Firaministan Burkina Faso Isaac Zida AFP PHOTO

Rundunar zaratan sojin fadar shugaban kasar Burkina Faso ta bukaci Firaministan kasar Isaac Zida ya yi marabus daga mukaminsa, wani abu da ake kallo a matsayin babbar baraka tsakanin sojoin kasar watanni uku bayan korar Blaise Campaore daga karagar mulki.

Talla

Duk da cewa babu cikakken bayanai a game da dalilan neman kanar Zida ya yi marabus daga mukaminsa, to amma manazarta al’amurran da ke faruwa a kasar ta yammacin Afirka na ganin hakan ba ya rasa nasaba da yunkurin Firaministan na ganin an rusa wannan runduna ta soji.

Majiyoyi sun ce ko a ranar 30 ga watan disambar da ya gabata, wasu manyan jami’an soji daga wannan runduna sun gana da Firaministan, inda suka bukaci ya ba su wasu mukamai kafin ranar 30 ga watan janairun da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.