Najeriya

An bai wa sarkin Kano Muhammadu Sanusi sandar girma

Mai Martaba sarkin Kano Mahammadu Sanusi na Biyu
Mai Martaba sarkin Kano Mahammadu Sanusi na Biyu

A jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, a wannan asabar an gudanar da kiin bada sandar girma ga maimartaba sarkin kano MUHAMMADU sunusi na biyu, inda hakan ke nuna an kammala tabbatar masa da sarautar Kanon a hukumance.

Talla

Gwamnan Kano Rabiu Musa kwankwaso ne ya mika wa sarkin sandar girma dama sauran kayan sarautar, kamar yadda yake bisa al'ada.

An dai gudanar da kasaitaccen biki a karkashin jagoranci Mai alfarma sarkin musulmi Sa’ad Abubakar na uku, da kuma halartar sarakunan gargajiya daga sassa daban na kasar.

Har ila yau akwa wasu baki daga ciki da wajen Najeriyar ciki harda tsoffin shugabannin kasar janar MUHAMMADU Buhari da janar Yakubu Gowon, da jakadan Amurka a Najeriya da dai sauransu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.