Burkina Faso-ECOWAS

Zanga-zangar adawa da sojoji a Burkina Faso

Matasa na zanga-zanga a birnin Ouagadougou na Burkina Faso
Matasa na zanga-zanga a birnin Ouagadougou na Burkina Faso RFI/Yaya Boudani

A yau asabar dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, inda suka bukaci a rusa rundunar zaratan sojin da ke gadin fadar shugaban kasar.

Talla

Kungiyoyin fararen hula ne suka bukaci a gudanar da zanga-zangar, bayan da a ranar laraba da ta gabata sojojin suka bukaci a tube Firaminista Isaac Yacouba Zida daga mukaminsa, kafin daga bisani sun janye wannan bukata tasu.

A cikin watan oktoban bara ne al’ummar kasar suka gudanar da tarzomar da ta yi sanadiyyar faduwar gwamnatin shugaban Blaise Compoare, bayan share shekaru 27 kan karagar mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.