Najeriya-Amurka

Amurka ta yi allawadai da dage zaben Najeriya

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama da Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama da Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry

Gwamnatin kasar Amurka ta yi allawadai da matakin dage zaben Najeriya har zuwa karshen watan Maris, tare da yin kira ga al’ummar kasar su kai zuciya nesa. A ranar Assabar ne Hukumar zaben Najeriya ta bayyana dage babban Zaben har zuwa nan da makwanni 6.

Talla

Shugaban hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega ya dage zaben ne bayan hukumomin tsaro a kasar sun ce ba za su iya tabbatar da tsaron rayukan Jami’an hukumar ba da masu kada kuri’a a lokacin zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Fabriru.

Amma a cikin wata sanarwa sakataren harakon wajen Amurka John Kerry yace kazanlandar ga lamurran hukumar zabe mai zaman kanta abin ki ne. Kerry ya bayyana fargaba ga gwamnati na kokarin fakewa ga matsalar tsaro domin dagula dimukuradiya a Najeriya.

A watan Jiya john Kerry ya kawo ziyara garin Lagos a Najeriya game da fatawar Amurka na ganin an gudanar karbabben zabe cikin kwanciyar hankali ba tare rikici ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.