Najeriya

Ba za mu yadda a sake dage zabe ba- Buhari

Janar Muhammadu Buhari Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya
Janar Muhammadu Buhari Dan takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya Reuters

Dan takarar shugaban kasa Jam’iyyar APC mai adawa a Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa da bacin ransa game da matakin dage ranar babban Zabe a Najeriya daga 14 ga watan Fabriru zuwa 28 ga watan Maris.

Talla

Janar Buhari yace Hukumar zabe mai zaman kanta ta dauki matakin ne saboda matsin lamba da ta fuskanta, hakan kuma ke nuna Gwamnati ta yi kazanlandan ga ‘Yanci da kundin tsarin mulki ya ba hukumar.

A jiya Assabar ne dai shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya bayyana dage zaben daga 14 ga wannan watan har zuwa 28 ga watan Maris, sakamakon shawararin da hukumomin tsaro a kasar suka ba hukumar na rashin tabbatar da tsaro ga Jami’anta.

Amma Dan takarar babbar Jam’iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari ya ce ba za su amince a sake dage zaben ba tare da yin kira ga magoya bayan shi su yi hankuri su kwantar da hankalinsu.

"Tun da hukumar zabe tace kundin tsarin mulki ya yadda a yi zabe kafin 29 ga watan biyar, tun da tsarin mulkin bai hana ba, to ba yadda za mu yi amma ba za mu yadda a sake dage zaben ba" a cewar Buhari.

Bayan dage zaben Kasar Amurka ta yi allawadai da matakin, tare da yin kira ga al’ummar kasar su kai zuciya nesa.

Sauti: Janar Muhammadu Buhari

A cikin wata sanarwa sakataren harakon wajen Amurka John Kerry ya ce kazanlandar ga lamurran hukumar zabe mai zaman kanta abin ki ne. Kerry ya bayyana fargaba ga gwamnati na kokarin fakewa ga matsalar tsaro domin dagula dimukuradiya a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.