Nijar

Nijar ta kafa dokar ta-baci a Diffa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kafa dokar ta-baci a Jihar Diffa, inda kungiyar Boko Haram ta fara kadadmar da munanan hare hare a kasar da ke makwabtaka da Najeriya. Matakin na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta samu amincewar majalisa akan bukatar tura sojoji don yaki da Boko Haram.

Dakarun Chadi a yankin Diffa da ke fada Boko Haram a Najeriya
Dakarun Chadi a yankin Diffa da ke fada Boko Haram a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Gwamnatin Nijar ta dauki matakin kafa dokar ne bayan Ma’aikatar tsaro ta bayyana fargaba game da yadda mutane suka fara tserewa a yankin Diffa saboda tsoron rikicin Boko Haram.

Rahotanni sun ce an rufe ofisoshin gwamnati da makarantu da wuraren sana’a yayin da mutanen yankin ke ficewa.

A makon jiya ne Mayakan Boko Haram suka fara kaddamar da hari a garin Bosso na Jihar Diffa amma dakarun Nijar sun fatattaki ‘yayan kungiyar tare da kashe sama da 200.

Amma Boko Haram ta sake kai harin kunar bakin wake tare da kai hari a gidan yarin Diffa.

Daruruwan mutanen Najeriya ne dai suka tsallaka zuwa Diffa da ke kan iyaka da Najeriya bayan sun gujewa gidajensu saboda hare haren Boko Haram.

A karshen mako kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da Benin da ke makwabtaka da Najeriya sun amince su kafa rundunar soji 8,700 domin yakar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI