Nijar-Najeriya

Zanga-zanga don nuna adawa da Boko Haram a Nijar

Kawancen jam’iyyun da ke kan karagar mulkin Jamhuriyar Nijar ya bukaci al’ummar kasar baki daya da su gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin kasar wadda ta kuduri aniyyar fada da mayakan Boko Haram da suka soma kai wa kasar hare-hare.

Shugaban Majalisar Dokokin Nijar lokacin da ya ziyarci garin Diffa
Shugaban Majalisar Dokokin Nijar lokacin da ya ziyarci garin Diffa RFI/Nicolas Champeaux
Talla

Jam’iyyun siyasar sun bukaci a gudanar da wannan zanga-zanga a ranar 17 ga wannan wata na Fabarairu a duk fadin kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Mahamadou Issifou ya bukaci al’ummar kasar da su mara wa sojoji da kuma sauran jami’an tsaron kasar baya a kokarin da suke na kare iyakokin kasar daga barazanar wannan kungiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI