Nijar

An cafke wani shugaban Boko Haram a Nijar

Sojojin da ke fada da Boko Haram
Sojojin da ke fada da Boko Haram RFI/OR

Jami’an tsaro a kasar Nijar sun cafke wani da ake zargi shugaban Mayakan Boko Haram ne a garin Diffa bayan sun kaddamar da samame a gidansa inda suka samu manyan makamai a gidan. An bayyana sunan mutumin a matsayin Kaka Bonou wanda ya yi kaurin suna wajen fataucin kayan sata.

Talla

Wata majiyar Soji a Nijar ta tabbatar da cafke Bonou tare da kama manyan makamai da suka hada da rokoki a gidansa da ke Diffa.

Makwanni biyu da suka gabata, mayakan Boko Haram sun kai hare hare a yankin Diffa da ke kan iyaka da Najeriya, lamarin da ya sa hukumomin Nijar suka kafa dokar ta-baci domin yakar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI