Sudan

Sudan ta kwace Jaridu 13

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir

Jami’an tsaro a Sudan sun yi wa wasu kamfanonin Jaridun kasar dirar mikiya inda suka kwace kwafin jaridu 13 da aka buga a yau Litinin. Babu kuma wani dalilin kwace Jaridun da Jami’an tsaron suka bayar kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Talla

‘Yan jarida da ke aikin yada labaran keta hakkin bil’adama a Sudan sun ce gwamnatin kasar ta dade tana kwace kwafin jaridu da suka buga labarin da ya saba wa ra’ayinta.

Editan Jaridar Al-Tayar, Osman Mirghani ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa Jami’an tsaro sun kwace kwafin jaridarsa ba tare da wani dalili ba.

Sauran Jaridun da aka kwace sun hada da Al-Rai al-Aam da Al-Intibaha da Akhir Lahza da Al-Ahram al-Youm da Awal al-Nahar da Al-Watan da Al-Sudani da Alwan, Al-Saiha da Al-Mijhar al-Siyasi da Al-Dar da kuma Hikayat.

Sudan dai na cikin kasashen da ke sahun gaba a rahoton Kungiyar Reporters without Borders wajen kuntatawa ‘yancin jarida a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.