Nijar

Zanga-zangar adawa da Boko Haram a Nijar

Al’ummar Jamhuriyyar Nijar sun kaddamar da zanga-zangar nuna adawa da ayyukan Boko Haram na Najeriya tare da nuna goyan bayansu ga jami’an tsaron kasar da ke yaki da Mayakan kungiyar. Da misalin Karfe 9 na safe ne dubban mutane suka fito domin fara zanga-zangar a Yamai.

Masu zanga-zangar adawa da Boko Haram a Nijar
Masu zanga-zangar adawa da Boko Haram a Nijar Kalla/facebook
Talla

Jam’iyyun siyasar Nijar da ke jagorantar mulki ne suka bukaci a gudanar da zanga-zangar.

Asumana Mahammadu, Sakataren yada labaran PNDS Tarayya ya shaidawa RFI Hausa cewa za su fito ne domin karawa Sojin kasar kuzari.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan shugaban Kamaru Paul biya ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen da ke makwabtaka da Najeriya su hada kai domin yakar mayakan Boko Haram da suka tsallaka zuwa Nijar da Chadi da Kamaru.

Yanzu haka Hukumomin Nijar sun ce sun kama mutane 160 da ke da alaka da Boko haram cikinsu har da wani jigon kungiyar da ake kira Kaka Bonou.

A lokacin da ya ke bayar da sanarwa a Kafar telebijin Babban jami’in rundunar yaki da ta’addanci a Nijar Kaftin Adili Toro ya ce Bounou da suka cafke yana da hannu wajen harin da aka kai garin Diffa.

Jami’an tsaro sun sun kaddamar da samame a gidan Bonou inda suka samu manyan makamai.

Kaka Bonou dai ya yi kaurin suna wajen fataucin kayan sata.

Makwanni biyu da suka gabata, mayakan Boko Haram sun kai hare hare a yankin Diffa da ke kan iyaka da Najeriya, lamarin da ya sa hukumomin Nijar suka kafa dokar ta-baci domin yakar Boko Haram.

Yanzu Haka daruruwan mazauna garin Diffa a Jamhuriyar Nijar ne ke tsere wa gidajensu zuwa Damagaram don kaucewa hare haren kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI