Boko Haram

Za mu dagula zabe a Najeriya- inji Shekau

Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram YouTube

Shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar shekau ya sha alwashin dagula zaben da za a gudanar a Najeriya a cikin wani sakon bidiyo da ya aiko a Twitter a ranar Talata bayan wasu munanan hare haren kunar bakin wake da mayakan shi suka kai a garin Biu inda mutane 38 suka mutu.

Talla

Shekau ya ce ko za su mutu za su dagula zabe a Najeriya wanda za a gudanar a ranar 28 ga watan Maris.

Wannan ne karon farko da kungiyar ta aiko da bidiyo a Twitter, a wani sabon salon na canza yadda kungiyar ke yada sakwanninta bayan nadar sakwannin baya a DVD.

A cikin bidiyon Shekau ya ce su suka kai harin Gombe.

Boko Haram dai na ci gaba da zama barazana a Najeriya bayan dage zaben kasar bayan Jami’an tsaro sun ce suna bukatar lokaci domin kawo karshe kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.