Nijar

Boko Haram: Sojin Nijar biyu sun mutu a Bosso

Sojojin Nijar suna karbar horo a yankin Diffa
Sojojin Nijar suna karbar horo a yankin Diffa REUTERS

Ma’aikatar tsaron Nijar tace wani bom da Mayakan Boko Haram suka dasa a karkashin kasa ya yi sanadin mutuwar akalla Sojojin kasar guda biyu a garin Bosso na Jihar Diffa a ranar Talata. Sojojin sun taka bom din ne da aka dasa, kuma mutane hudu suka samu rauni.

Talla

Sanarwar ta bayyana cewa wannan ne karon farko da ‘Yan Boko Haram suka dasa wa Sojojin bom a yankin Diffa.

Nijar dai na fuskantar barazanar Boko Haram ne a yankin Diffa da ke makwabtaka da Najeriya.

Chadi da Nijar da Kamaru da ke bakwabta da Najeriya sun kaddamar da yaki domin kawo karshen Mayakan Boko Haram da ke yin barazana ga kasashen na yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI