Mali

Sarkin Abzinawan Kidal yana adawa da ballewar arewacin Mali

Sabon Sarkin Abzinawan Kidal da ke Arewacin Mali Mohammed Ag Intalla ya bayyana rashin amincewarsa da ballewar yankin don samun kwarya kwaryar ‘yanci, matakin da ake ganin ya yi karo da matsayin jama’arsa. Sarkin wanda ya gaji mahaifin sa a watan Disamba yace shi baya goyan bayan duk wani shiri na ballewa daga mali.

Askawan Mali da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kidal
Askawan Mali da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kidal Des soldats de la Minusma montent la garde devant le gouvernorat
Talla

Basaraken ya ce a shirye ya ke ya kaddamar da rangadin Yankunan Arewacin kasar don wanzar da zaman lafiya.

‘Yan tawayen Abzinawan Mali dai na son ‘yancin gashin kai ne a arewacin Mali, lamarin da ya sa suka kwace ikon yankin a lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta amadou Toumani Toure.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI