Masar-Amurka

Kerry na ziyara Masar akan batun IS

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry
Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry REUTERS/Evan Vucci/Pool

Sakataren harkokin wajen Amurk John Kerry ya isa kasar Masar, inda zai gana da Abdel Fattah al-Sisi don duba yadda za a tunkarin mayakan IS da ke da’awar Jihadi a duniya. Mr Kerry zai kuma gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da Sarki Abdulla na Jordan.

Talla

Shugabannin za su tattauna kan batutuwan da suka shafi matsalar tattalin arziki da ke damun hukumomin Falasdinawa.

A watan Junairu kasar Isra’ila ta rike kudaden da suka kai Dalar Amurka Miliyon 127, mallakin hukumomin Falasdinu saboda sun yi yunkurin shiga kotun hukunta manyan kaifuka ta duniya ICC.

Sannan Kerry zai tattauna batun barazanar IS da yadda Amurka za ta taimaka a murkushe mayakan da suka tsallaka zuwa Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.