Ebola

WHO: Ebola ta kashe mutane 10,000

Kasar Liberia ta bayyana sallamar mutum na karshe da ake kula da shi a Asibiti bayan gwaji ya nuna ba ya dauke da Ebola.
Kasar Liberia ta bayyana sallamar mutum na karshe da ake kula da shi a Asibiti bayan gwaji ya nuna ba ya dauke da Ebola. RFI/Sébastien Nemeth

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa zuwa yanzu fiye da mutane 10,000 ne suka mutu cikin mutane 24,000 da suka kamu da cutar cutar Ebola, a kasashen yammacin Afrika. Cutar ta fi yin kisa a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.

Talla

Wasu 6 sun mutu a Mali, guda a Amurka yayin da 8 suka rasa ransu a Najeriya, inda aka yi hanzarin kawar da cutar.

Rahoton hukumar ya ce akwai mutum guda mai dauke da cutar a Senegal da Spain, amma babu rahoton mutuwa a kasashen.

A kasar Saliyo an bayyana cewa adadin mutane 11,677 suka mutu, a Liberia kuma 3,655, a Guinea mutane 2,187 suka mutu.

Amma a makon jiya ne kasar Liberia ta bayyana sallamar mutum na karshe da ake kula da shi a Asibiti bayan gwaji ya nuna ba ya dauke da Ebola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.