Najeriya

Buhari ya bayyana aniyar fada da Boko Haram

Janar Muhammadu Buhari
Janar Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER

Jim kadan bayan da ya lashe zaben shugabancin kasar da kasashen duniya suka yaba wa, zababben shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa na daura yaki da 'yan kungiyar Boko Haram

Talla

Saban Shugaban Kasar da ya ka da shugaba Jonathan da ke kan karagar mulki ya bayyana cewa sai da tsaro kowace kasa a duniya ke samun ci gaba.

A lokacin yakin neman zabensa dai, Janar Buhari ya dau wa al’umar Najeriya alkawarin yaki da matsalar rashin tsaro da kuma cin hanci da rashawa da suka zame wa kasar tamkar cututukan da ba su da magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI