Najeriya

Harin bom ya kashe mutane 5 a Gombe

Wani harin bom da aka taba kai wa a Gombe
Wani harin bom da aka taba kai wa a Gombe REUTERS/Afolabi Sotunde

Wani Bom da ya fashe a kusa da tashar mota a garin Gombe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya a jiya Alhamis, ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da raunata wasu da dama. Rahotanni sun ce wata Mata ce ta ajiye bom din a tashar motar.

Talla

An kai harin ne bayan an idar sallar Isha’i a jiya Alhamis.

Wani jami’in kungiyar direbobi a jihar Gombe Muhammadu Garkuwa ya shaidawa Kamfanin dillacin labarun Faransa cewa Matar ta ajiye jikarta da ke dauke da Bom din a kusa da wata motar bus da ke lodin Jos.

Harin ya yi kama da irin hare haren da Kungiyar Boko Haram ke kai wa a arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.