Kenya-Somalia

Mayakan al-Shebab sun aika wa Kenya sabuwar barazana

Wani sojan kasar Kenya, a jami'ar da mayakan al-Shebab suka kai hari
Wani sojan kasar Kenya, a jami'ar da mayakan al-Shebab suka kai hari AFP PHOTO / CARL DE SOUZA

Yau Asabar ‘yan Sandan kasar Kenya sun nuna wa jama’a wasu gawarwakin mayakan al-Shebab da suka kashe kusan m,utane 150, sakamakon wani harin da suka kai a wata jami’ar kasar. Matakin na ‘yan sandan na zuwa ne jim kadan bayan ‘yan kungiyar ta al-Shebab masu alaka da al-Qaeda, sun aike da wani sako, inda suke barazanar sake kai hare hare a kasar.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin kasar ta Kenya suka bayyana shirnin yin zaman makoki na kwanaki 3, don gudanar da addu’a ga mutane da suka mutu sakamakon harin.Shugaba Uhuru Kenyatta, daya bayar da sanarwar yace za a yi kasa da tutocin kasar a tsawon kwanakin, inda kuma ya bayyana harin da dabbanci.Wannan ne karon farkon da shugaba keyatta ke jawabi ga ‘yan kasar, tun bayan harin na ranar Alhamis, da aka bayyana a matsayi daya daga cikin mafi muni a kasar.