Boko Haram ta budewa mutane wuta a kauyukan Borno
Wallafawa ranar:
Rahotanin daga Jihar Bornon Najeriya sun ce wasu da ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Kwajaffa, dake karamar hukumar Hawul, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama
Mazaunar garin Sun tabbatar da cewar an kai harin ne a daren jiya Lahadi, kuma an kona wasu sassan garin.
Ahmed Ali na daya daga cikin mazauna garin, wanda ya shaidawa kamfanin dilanci labaran faransa cewar, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun tara mutane wuri guda, suka yi musu wa'azi, sannan daga bisani suka kashe su.
Kazalika, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari a kan wasu kauyuka da ke karamar hukumar Kala Balge.
Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka mutu a wuraren da aka kai hare-haren ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu