Malawi

An umarci 'yan Sandan Malawi su harbi masu kashe Zabiya a kasar

Wani yaro Zabiya da aka kaiwa hari
Wani yaro Zabiya da aka kaiwa hari

Hukumomi a Malawi su umarci ‘yan sandan kasar su harbe duk wanda suka samu hannu dumu dumu wajen kai harin kan masu cutar zabiya, da nufin sayar da sassan jikinsu don yin tsafi. Shugaban ‘yan sandan kasar Lexen Kachama ya bayyana masu irin wannan halin da cewa suna aikata mummunan lafi.Shugaban ‘yan sandan Lexen Kachama, dake magana a yankin Machinga na kudancin kasar ta Malawi, yace ba zasu sa ido ana ci gaba da hallaka zabiya ba kamar dabbobi.Kachama yace baya so ya sake jin an ce dan sanda na fafurar masu aikata wannan laifin, dauke da barkonon tsohuwa ko karamamin makami.Shugaban ‘yan Sandan yace so yake yi yaga an yi amfani da makami daidai da lafin da mutum ya aikata, don ganin al’umma sun tsira daga miyagun mutane, saboda doka ta basu damar yin hakan.Kungiyar masu zabiya a kasar Malawi, ta bayyana cewa an kashe mata mutane 6 cikin kasar, daga watan Disamba zuwa yanzu.A cikin ‘yan watannin nan, zabiya suna fuskantar hare hare a sassan nahiyar Africa da dama, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa lamarin ya fi kamari a kasashen Tanzania, Burundi da Malawi.Majalisar ta Dinkin Duniya tace ta’azzara da matsalar tayi a Tanzania, bai rasa nasaba da zaben shugaban kasar da za ayi cikin watan Oktoba, lamarin daya sa ‘yan siyasa ke bin matsafa don samun nasara.