Najeriya

Boko Haram ta kai hari a kauyen Dile Jihar Borno

Wani hari da Boko Haram suka kai a garin Benisheik a Jahar Borno a Najeriya
Wani hari da Boko Haram suka kai a garin Benisheik a Jahar Borno a Najeriya REUTERS/Stringer

Mayakan kungiyar Boko Haram sun bude wa mutane wuta a kauyen Dile da ke kusa da garin Askira Uba a Jihar Borno inda suka kashe mutane sama da 20 tare da kona gidaje da dukiyoyin Jama’a. Rahotanni sun ce mayakan sun kai farmaki a kauyen ne a jiya Alhamis da rana.

Talla

Wasu mazauna garin da suka tsira da ransu a garin sun ce mayakan sun shigo kauyen cikin motoci sanye da rawani suna Kabbara tare da budewa mutane wuta.

Wani mazauni Askira Uba ya ce babu jami’an tsaro a yankin a lokacin da Mayakan suka kawo hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.