Hukumar lafiya ta duniya ta gargadi Afrika a kan Ebola
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta gargadi hukumomin kasashen Afrika don ganin sun zage dantse tareda bada kulawa da ta dace, wajen yaki da cutar Ebola
Hukumar ta WHO, tayi gargadin ne a lokacin wani taron manema labarai, a birnin Geneva na kasar Swizerland
Shugaban cibiyar yaki da kamuwa da cutar Ebola dake aiki da hukumar lafiya ta Duniya OMS,Dr. Bruce Aylward, ya sanar cewa ana cigaba da bicinken gano allurar kariya da magugunan da suka dace domin yakar cutar ta Ebola a wasu kasshen Afrika.
Dr Aylward ya tabbatar cewa hukumar ba za ta dakatar da bayar da gudumuwa ga kwararun dake cigaba da gudanar da bicinke duk da yake ya zuwa yanzu da sauren aiki a wasu wuraren, ganin yadda mutane ke cigaba da kaucewa bin umurni jami’an kiwon lafiya.
Hukumar lafiya ta Duniya a wani rahoto da ta fitar ta sanar da manufofinta, da suka hada da hanyoyin da suka dace abi domin kiyaye kamuwa da wanan cuta.
A wasu alkaluma da hukumar ta fitar ta sanar da irin yadda aka samu kusan kashi 50 cikin 100 na yawan mutane da suka sake kamuwa da wanan cuta ta Ebola.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu