Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun kwato wasu garuruwan Yobe da Borno

Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram REUTERS/Joe Penney
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da karbe wasu garuruwa daga hannun mayakan Boko Haram a Jihohin Barno da Yobe da suka hada da Bita da Isge da Yamteke da Uba a kananan hukumomin Askira Uba da Damboa a Jihar Barno da kuma Buni Yadi a Jihar Yobe.

Talla

Daraktan yada labaran sojin Kanan Sani Usman Kukasheka ne ya tabbatar da haka tare da cewar sojojin runduna ta 3 da runduna ta 7 suka samu nasarar fafatawar da suka yi jiya.

Kanal Usman ya ce sun rasa soja guda a aikin yayin da wasu 10 suka samu raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.