Najeriya

Ba zan yi alkawalin karbo Matan Chibok ba-Buhari

Janar Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya mai jiran gado
Janar Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya mai jiran gado

Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi alkawalin kubutar da ‘Yan Matan Chibok 219 ba da mayakan Boko Haram suka sace saboda har yanzu ba a san inda ake garkuwa da su ba. Buhari ya fadi haka ne a yau Talata da ake juyayin cika shekara guda da sace ‘Yan matan.

Talla

A cikin sanarwar da ya fitar, Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta domin mika ‘Yan matan ga iyayensu.

A ranar 14 ga watan Fabrairun bara ne mayakan Boko Haram suka abka wa makarantar mata a garin Chibok cikin Jihar Borno tare da  sace ‘Yan mata 276 a lokacin da suke shirin rubuta jarabawa.

An dade rundunar Sojin Najeriya na ikirarin cewa ta san inda ake garkuwa da ‘Yan matan Chibok, amma tana fargaba akan tsoron kada a kashe su wajen kubutar da su.

Batun sace ‘Yan matan dai na daya daga cikin dalilan da suka janyo wa gwamnatin Goodluck Jonathan bakin jini a Najeriya, inda ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris.

Jonathan ya dade yana alkawalin kubutar da ‘Yan matan ba tare da wani sharadi ba.
Amma Buhari da ya kayar da Jonathan a zaben shugaban kasa ya ce akwai bukatar fadin gaskiya akan makomar ‘yan matan da kuma yaki da Boko Haram.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta wallafa rahoto da ke cewa akalla mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon shekarar da ta gabata.

Amnesty tace mayakan Boko Haram suna lalata da wasu ‘yan matan, tare da tursasa mu su daukar makamai.

Buhari ya ce yau rana ce ta bakin jiki da jimami akan halin da ‘yan matan da iyayensu ke ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI