Tunisiya
Tunisya Na Daukan Matakan Kare Baki
Wallafawa ranar:
Hukumomi a kasar Tunisia na daukan matakan kare baki da masu yawon shakatawa dake son zuwa kasar wannan lokacin, ganin yadda masu jihadi suka kashe baki 21 watan jiya a ziyarar da 'yan yawon bude idanu ke kaiwa.Bakin ‘yan yawon bude ido na daga cikin kafofin samun kudaden shiga na Gwamnati.Shugaban kungiyar masu otel-otel da masaukin baki dake kasar Radhoune Ben Salah ya fadi cewa suna iyakacin kokarin ganin wannan zuwar baki kasar anyi ta lami lafiya.