Nigeria

Sojan Nigeria Na Samun Nasara Kan Boko Haram

wasu mata da aka sace masu yara a garin Chibok
wasu mata da aka sace masu yara a garin Chibok Reuters/Afolabi Sotunde

Hedkwatan tsaro na Nigeria ta ce tana ta samun nasarar kubutar da mata da yara kanana da ‘yan kungiyar Boko Haran suka sace zuwa dajin Sambisa.Na baya-bayan tace an kubutar da mutane 234 daga Dajin na Sambida a kan hanyar Konduga da kawuri a jihar Borno.Tunda fari dai an sanar da kubutar da mata da yara kusan 500 daga wannan daji.Sai dai babu bayanin ko 'yan matan makarantar Chibok da aka sace shekara daya daya gabata na daga cikin wadan da aka kubutar.