Nigeria

Sojan Nigeria Ta Ce Saura Kiris Ta Kawo Karshen Boko Haram

Wasu sojan Nigeria na farautar 'yan kungiyar Boko Haram
Wasu sojan Nigeria na farautar 'yan kungiyar Boko Haram AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

Rundunar tsaro ta Nigeria ta ce mayakan kungiyar Boko Haram na kusan shiga hannu domin anyi masu kofar rago yanzu haka a dajin Sambissa, amma babban abin da ya sa aka ki afka masu ta kasa shine fargaban nakiyoyi da suka daddasa.Major-General Chris Olu Kolade ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Reuters cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun yiwa harabar inda aka rutsa su zobe da nakiyoyi a yanzu haka.A watan jiya ne dai Sojan Nigeria suka kaddamar da hare-hare a dajin na Sambisa, inda ake kyautata zaton wani mutun dake fitowa jefi-jefi ta Video yana maganganu yake boye, wata kila da ‘yan matan nan samada 200 na sakandaren Chibok da kungiyar ta sace samada shekara daya daya gabata.Tun kwanakin baya ne dai Shugaban Nigeria mai barin gado Goodluck Jonathan ya umarci akamo shi jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da ransa.Rundanar Sojan Nigeria ta ce tana samun nasara kan kungiyar Boko Haram domin ta kubutar da mata da yara da yawa.