Nijar

‘Yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali a tafkin Chadi

Sansanin 'Yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya
Sansanin 'Yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da Jinkai a Nijar, yace adadin mutane 25,000 da suka gudu daga yankin Tafkin Chadi zuwa garuruwan N’Guigmi da Bosso domin tsira daga hare haren Boko Haram suna cikin mawuyacin hali.

Talla

Wani jami’in Majalisar da ya isa garin ya bayyana halin da ya ga mutanen a matsayin abin takaici, inda yace wasu daga cikinsu na zama a sararin Allah, cikin tsananin rana babu matsuguni.

Jami’in ya ce Mata da yara kanana na fuskantar matsalar rashin ruwan sha.

Rahotanni sun ce ziyarar da Firaminista Briji Rafini ya kai N’Guigmi ya sa an fara rabawa baki 12,000 hatsi don samun abinda za su sa a baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI