Liberia-Ebola

Liberia ta rabu da Ebola-WHO

Shugaban Amurka Barack Obama da Shugabar Liberia Johnson Sirleaf
Shugaban Amurka Barack Obama da Shugabar Liberia Johnson Sirleaf REUTERS/Larry Downing

A yau assabar Hukumar Lafiya ta duniya WHO, ta tabbatar da cewa babu sauran cutar Ebola a Liberia, bayan daukan tsahon kawanaki 42 ana sa’ido ba tare da an samu wani wanda ya kamu da cutar ba.

Talla

Sai dai WHO ta gargadi cewa kar a sakankance domin har yanzu akwai sauran cutar a makwabtan kasar ta Liberia, wato Guinea da Saliyo.

Shugabar Liberiar Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana farin ciki ta akan wannan nasara

Fiye da shekara guda da ta wuce ne kasar ta Liberia ta ba da rahoton kamuwa da cutar a karo na farko bayan cutar ta yadu daga Guinea.

Tuni kasar Amurka ta aikawa Liberia sakon taya murna akan wannan cigaba da aka samu

Cutar ebola dai tayi ajali mutane sama da dubu 4 a liberia
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI