Yemen-Djibouti

Shugaban kasar Djibouti yayi gargadi kan yakin basasan kasar Yemen

Shugabana kasar Djibouti, Ismaïl Omar Guelleh
Shugabana kasar Djibouti, Ismaïl Omar Guelleh AFP Photo/Thierry Charlier

Shugaban kasar Djibouti yayi gargadin cewa yakin basasan da ake gwabzawa a kasar Yeman, da kuma kokarin farfadowar da kungiyar Al-Qaeda keyi, na matsayin babbar barazana ga yankin gabas ta tsakiya. Sai dai shugaba Ismail Omar Guelleh ya yi alkawarin ci gaba da baiwa ‘yan gudun hijira dake tserewa daga rikicin Yemen din tallafin da suke bukata.Shugaba Guelleh, dake hira da kamfanin dillacin labarun Faransa na AFP, yace yakin na Yemen, dake daya bangaren da teku da ta raba kasar da Djibouti, a yankin kahon Africa, ya haddasa kiyayya mai tsanani tsakanin mabiya Sunni da Shi’a, lamarin dake zama babbar barazana ga yankin.