Chadi-Najeriya

Chadi na da sabani da Najeriya akan Boko Haram

Shugaba Goodluck Jonathan da Shugaba Chadi Idriss Déby
Shugaba Goodluck Jonathan da Shugaba Chadi Idriss Déby AFP PHOTO / BRAHIM ADJI

Shugaban kasar Chadi, Idris Deby ya ce rashin hada hannu waje guda, na kawo cikas wajen samun nasara dakile ayukan Kungiyar Boko Haram. Deby ya fadi hakan ne a wata ziyara da ya kawo Najeriya a yau litinin.

Talla

Jim kadan bayan ganawarsa da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a cikin sirri, a Abuja Deby ya ce rashin hadin gwiwa tsakanin sojoji Najeriya da Chadi ya kawo tsaiko a yakin kawar da Boko Haram Wakilin RFI Hausa Muhammad Kabir Yusuf ya aiko da rahoto daga Abuja.

Rahoto: Chadi na da sabani da Najeriya akan Boko Haram

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.