Najeriya

Sojoji sun kafa dokar hana fita a Maiduguri

Titin  Kashim Ibrahim a garin  Maiduguri Jihar Borno a Najeriya
Titin Kashim Ibrahim a garin Maiduguri Jihar Borno a Najeriya AFP PHOTO / STRINGER

Sojojin Najeriya sun kafa dokar hana fita ta sa’o’I 24 a garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabaci, bayan sojojin sun fafata da mayakan Boko Haram wadanda suka kaddamar da hari a jiya Laraba.

Talla

Kakakin rundunar Sojin a Maiduguri Kanal Tanko Gusau wanda ya bayar da sanarwar ya ce sun kafa dokar ne don kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Maiduguri.

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari ne a daren Laraba a Maiduguri amma Sojin Najeriya sun nasarar korarsu daga garin bayan sun yi musayar wuta.

‘Yan bindigan dake dauke da muggan makamai, sun farwa yankunan da ke kusa da wani barikin soja, inda suka yi ta harbe harbe ba kakkautawa.

Mazauna garin sun ce bayan sun kamala sallar Magariba ne suka ji karar fashewa da harbin bindigogi.

Sai dai rundunar Sojan kasar tace wasu mata ‘yan kunar bakin wake ne suka yi yunkurin tayar da bama bamai a birnin, inda dakarun kasar suka shawo kan lamari.

Mukaddashin Dakaraktan yada labaru na rundunar Sajan kasar, Kanal Sani Usman Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa cewa wasu mata ne suka yi kokarin kai harin Kunar bakin wake a Maiduguri.

Kanal Sani ya ce sun yi kokarin shawo kan ‘Yan ta’addan cikin lokaci kankani.

Majiyoyin Soji da mazauna yankin Borno sun ce kimanin Mutane 9 aka kashe a musayar wutar Maiduguri.

Wani shugaban ‘Yan kato da gora Yusuf Sani ya ce sojoji uku aka kashe da wasu ‘Yan kato da gora guda shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.