Isa ga babban shafi
Masar

An zartar da hukuncin kisa kan mutane 6 a kasar Masar

Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed

Yau lahadi, hukumomin kasar Masar suka zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane 6, da aka yanke musu hukuncin, bayan da aka same su da laifin kashe sojojin kasar. Hukumomin na birnin Alkahira sun sa kafa suka yi fatali da kiraye kirayen da aka yi ta yi, na neman afuwa ga mutanen, bayan da wata kotun soja ta tabbatar da hukuncin.Dun wannan na zuwa ne bayan da rahotani ke cewa 2 daga cikin mutanen da aka yanke musu hukuncin, suna tsare a hannun jami’an tsaro, lokacin da aka aikata laifin. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.