Afrika ta Kudu

Rashin wutar lantarki na barazana ga tattalin arziki

Shugaban afrika ta kudu Jacob Zuma.
Shugaban afrika ta kudu Jacob Zuma. Reuters/Nic Bothma/Pool

Ministar kudi a kasar afrika ta kudu Nene Nhlanhla ta ce matsalar wutar lantarki na cigaba da zama babba nakasu ga cigaba tattalin arziki a afrika ta kudu, musamman a Masana’antu, da offisoshi sassan kasar.A zantarwata da manema labarai a Johannesburg Nene ta ce, anyi hasashen samun habbaka acikin wannan shekara da kashi 2 cikin 100 na tattalin arziki, kasa da abin da ake tsamanin domin rage matsalolin rashin ayukan yi, da kuma ceto matasa daga damuwa musamma bakaken fata.

Talla

Nene dai ta bayyana damuwarta cewa in dai al’amura ba su dai-daita wannan matsala ka iya jefa kasar acikin wani hali na tattalin arziki, lura da yadda masana’antu da dama ke balaguro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.