Burundi

Cutar Amai da gudawa ta barke a sansanin ‘yan Burundi a Tanzania

Sansanin da ake kula da lafiyar 'yan gudun hijirar kasar Burundi a Tanzania
Sansanin da ake kula da lafiyar 'yan gudun hijirar kasar Burundi a Tanzania REUTERS/Thomas Mukoya

Gwamnatin Tanzania ta tabbatar bullar cutar amai da gudawa a sansanin ‘yan gudun hijirar kasar Burundi, wadanda suka gudu sakamakon rikicin siyasar da ake fama da shi a kasarsu. Ministan kiwon lafiya a kasar Tanzania Nsachris Mwamwaja, ya ce gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa cutar kwalara ce ta bulla a sansanin da ke kunshe da dubban ‘yan Burundi.

Talla

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da ‘yan Burundi 100,000 suka fice kasar zuwa makwabta bayan barkewar zanga-zangar adawa da matakin shugaba Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

Hukumar ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen Burundi 70,200 suka tsere zuwa Tanzania, 26,300 suka tsallaka zuwa Rwanda, yayin da 10,000 suka shiga kudancin Kivu a kasar Jamhuriyyar Congo.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta yi kira ga bangarorin da ke rikici a kasar su kai zuciya nesa don gujewa abkawa yakin basasa.

Yanzu haka ‘Yan adawa sun bukaci Shugaba Nkurunziza ya yi murabus tare da bijirewa gwamnatinsa na kawo karshen zanga-zangar da aka shafe makwanni ana yi a Bujumbura.

Akalla mutane 20 suka mutu tun barkewar zanga-zangar a watan Afrilu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI