Nijar

Hukumomin Nijar sun dakatar da Shugaban Alternative

Moussa Tchangari Shugaban Alternative Citoyen a Nijar
Moussa Tchangari Shugaban Alternative Citoyen a Nijar

A jamhuriyar Nijar rundunar yaki da ayyukan ta’addanci ta kasar na tsare da Moussa Tchangari wani shahararren dan gwagwarmaya kuma shugaban cibiyar wayar da kai da kare hakkin Bil’adama ta Alternative Espaces Citoyens.

Talla

Bayanai sun ce an kama Changari ne lokacin da ya je cibiyar domin kai wa wasu mutane abinci cikinsu kuwa har da sarakunan gargajiya da aka kama a jihar Diffa sannan kuma ake tsare da su a birnin Yamai bisa zargin cewa ba sa bayar da hadin kai a yakin da kasar ke yi da ayyukan ta’addanci

A cikin shirinmu na safiyar jiya, Moussa Changari ya bukaci hukumomin kasar da su gaggauta sakin wadannan mutane.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.