Najeriya

APC za ta tattauna alkiblar gwamnatin Buhari

Jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu tare da Zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari
Jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu tare da Zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari REUTERS

Jam’iyyar APC da ke shirin kama aiki a Najeriya za ta bayyana manufofinta da alkiblar gwamnatin shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da za a fara a yau Laraba a Abuja.

Talla

“Samar da Canji a Zahirance” na daga cikin manyan batutuwan da taron zai tattauna.

Malam Nasir El Rufa’I Zababben gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Abuja, na daga cikin mambobin kwamitin da ke jagorantar taron, kuma ya shaidawa RFI Hausa cewa taron ya kunshi tattaunawa akan yadda zasu cika alkawullan gwamnatinsu ga ‘Yan Najeriya.

Taron zai kunshi zababben shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da Gwamnonin Jam’iyyar APC da ‘Yan Majalisu.

El Rufa’I ya ce taron kamar tunatarwa ce ga shugabannin da aka zaba na APC game da yadda za su cika alkawullan da suka dauka.

A ranar Juma’a 29 ga watan Mayu, Muhammadu Buhari zai karbi ragamar shugabancin Najeriya daga hannun Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP da ta sha kaye a zaben watan Maris bayan ta shafe shekaru 16 tana shugabanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.