Najeriya

Daga ina Buhari zai fara ?

Zababben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Zababben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari opinionnigeria.com

A ranar Juma’a ne za a rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Najeriya, amma zai gaji gwamnati ne a lokacin da Najeriya ke cike da matsaloli a fannoni da dama. Babban kalubale da ke gabansa shi ne cika alkawullan da Jam’iyyarsa ta APC ta dauka na tabbatar da canji a kasar.

Talla

Akwai manyan kalubale guda hudu da Buhari zai yi kokarin tunkara idan an rantsar da shi a ranar Juma’a.

Rashawa.

Buhari wanda tsohon shugaban kasa ne a zamanin mulkin Soja a 1980, ya nanata cewa sabuwar gwamnatinsa ba za ta yi cudanya da rashawa ba da bara-gurbi.

Akwai hukumomin gwamnati da dama da ke bukatar sauyi da suka hada da kamfanin Mai na NNPC. Kuma masu sharhi na ganin Buhari zai yi tankade da rairaya a NNPC.

Domin yaki da Rashawa, tuni Buhari ya yi alkawalin bayyana kadarorinsa da duk wanda zai karbi mukami a gwamnatinsa.

Ana ganin Buhari zai inganta hukumomin da ke yaki da rashawa a Najeriya.

Tsaro

Rashin magance rikicin Boko Haram na daya daga cikin matsalolin da suka kawo karshen gwamnatin Goodluck Jonathan na PDP.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 15,000 suka mutu yayin da sama da mutane Miliyan guda da rabi suka gujewa gidajensu saboda rikicin Boko Haram.

Dole sai Buhari ya tabbatar da tsaro a Najeriya kafin samun ci gaban tafiyar da gwamnatinsa.

Buhari wanda tsohon Soja ne ya jaddada cewa zai jagoranci Yaki da Boko Haram tare da samar da wani tsari da zai karfafawa Sojoji guiwa  da magance rashawa da ta dabaibaye rundunar sojin Najeriya.

Kamaru da Chadi sun fito suna zargin gwamnatin Jonathan na rashin bayar da hadin kai domin kawar da ayyukan Boko Haram da ya shafi kasashen da ke kusa tafkin Chadi.

Buhari ya ce zai inganta huldar Najeriya da Chadi da Nijar da Kamaru wadanda suka kaddamar da yaki akan Boko Haram.

Bakonmu: Barr Solomon Dalung

Rashin Ayyukan yi.

Akalluma sun nuna cewa kusan kashi biyu cikin uku na al’ummar Najeriya sama da miliyan 170 ‘yan kasa da shekaru 30 ne, kuma alkalumma sun nuna cewa kusan kashi 30 matasa ne ke zaman kashe wando.

Jam’iyyar APC tace kimanin mutane Miliyan 110 ne ke fama da talauci a Najeriya. Amma gwamnatin Buhari ta yi alkawalin fito da wani sabon shiri da zai magance matsalar ta hanyar farfado da masana’antu da gina hanyoyi tare da samar da wutar lantarki.

Sai dai kuma masu sharhi na ganin matsalar faduwar farashin mai na iya kawo wa Buhari cikas wajen samun kudaden da za a gudanar da ayyukan ci gaba a Najeriya.

Wutar Lantarki

Domin samar da ayyukan yi da ci gaban masana’antu, matsalar wutar lantarki na daga cikin muhimman fanononi da Gwamnatin Buhari ya kama ta mayar da hankali akai.

Zaben 2015 a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.