Najeriya

Buhari zai halarci taron G7 a Jamus

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci taron kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki da za a gudanar a kasar Jamus. Kakakinsa Shehu Garba ya ce Buhari zai bar Najeriya a ranar Lahadi domin halartar taron.

Sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Firaministan Birtaniya a London
Sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Firaministan Birtaniya a London REUTERS/Neil Hall
Talla

A lokacin da ya ziyarci Najeriya wajen bikin rantsar da Buhari a ranar Juma’a, Ministan harakokin wajen Birtaniya Philip Hammond ya shaidawa sabon shugaban cewa Firaministan Birtaniya David Cameron yana son ya halarci taron G7 tare da zuwa da bukatun Najeriya.

Shehu Garba ya ce shugaba Buhari ya amince da goron gayyatar, kuma zai kai ziyarar kwanaki biyu a Jamus.

A ziyarar da Buhari ya kai Birtaniya kafin bikin rantsar da shi, David Cameron ya nemi goyon bayansa kan inganta huldar cinikayya tsakanin Kungiyar Turai da Afrika tare da yin alkawalin taimakawa Najeriya kan bukatunta na kokarin kawo karshen yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI