Congo-britain

Congo ta zargi kamfanin Britaniya da cin hanci

Dallar Amurka
Dallar Amurka Getty Images/Blackwaterimages

Wata Kungiyar kare hakkin Bil’adama a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta zargi wani Kamfanin mai na Britaniya, wato Soco International, da laifin karban cin hanci.

Talla

Kungiyar kare hakkin bil’adama mai suna Global Witness ce ta zargi kamfanin SOCO da laifin karbar cin hanci domin ta rufe bakin jama'a dake sukan aikin tonon mai da suke yi a kasar.

Kungiyar ta gabatar da kwafin checque na kudaden banki da kamfanin man na Britaniya ya bayar cin hancin na kudin Amirka Dolla dubu 15 da dari shida.

Kungiyar na cewa akwai kuma wasu hujjojin na biyan makudan kudade na cin hancin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.