Masar

Kotu ta Jinkirta Hukuncin Kashe Mutane 16 da suka Kashe 'Yan Sanda 25

Sojan kasar Masar a bakin aiki.
Sojan kasar Masar a bakin aiki. AFP PHOTO / MOHAMED EL-SHAHED

Wata kotu a kasar Masar ta umarci sake duba zargi da ake yi wa wasu mutane 16 na kisan ‘yan sanda 25 a yankin Sinai, bayan da aka zartas masu da hukuncin kisa, wasun su kuma dauri na tsawo rayuwa gidan maza. 

Talla

Mutanen 16 na daga cikin mutane 35 da ake zargi da kaiwa wata mota dauke da ‘yan sanda harin gurneti cikin watan takwas na shekara ta 2013 inda aka kashe ‘yan sanda 25.

A zaman  kotun yau Asabar, an nemi a sake bincike da shigar da kara na mutanen da aka zartas masu da hukuncin kisa.

Kotun ta lura cewa akwai kura-kurai wajen shigar da karar tun da fari.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI