Egypt

Kotu ta tabbatar da hukuncin kisa a kan Morsi

Tsohon shugaban kasar Masar Muhamed Morsi
Tsohon shugaban kasar Masar Muhamed Morsi REUTERS

Kotu Masar ta tabbatar da hukuncin kisa akan hambararan shugaban kasar, Muhammed Morsi akan laifin hannu wajen fasa gidan yari da kuma harin da aka kai wa 'yan sanda, a boren da aka yi a shekarar 2011 na hambarar da Hosni Mubarak.

Talla

Hukuncin kotun na yau Talata ya biyo bayan tattaunawa da babban Mufti na Masar domin ya fayyace dokar Musulunci a kan hukuncin.

Kafin wannan hukuncin dai, sai da aka fara yanke masa hukuncin daurin rai da rai da farko bayan samun sa da laifin leken asiri.

Haka kuma an yanke wa wasu manyan Jami'an kungiyar ‘yan uwa Muslim hukuncin kisa saboda yi wa kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma Hezbollah ta Lebanon da kuma kasar Iran leken asiri.

Morsi dai na da daman daukaka kara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI