Masar

Azhar ta soki cin zarafin musulunci da aka yi a kasar Holland

Wani taron malaman Azhar dake Masar
Wani taron malaman Azhar dake Masar REUTERS/Al Youm Al Saabi Newspaper

Jami’ar Al Azhar dake kasar Masar tayi Allah wadai da hotan da wata tashar talabijin dake kasar Holland ta nuna wanda ta danganta shi  da Manzan Allah tsira da amincin Allah su kara tabbatat a gare shi.

Talla

Sanarwar da jami’ar ta bayar ta bukaci al’ummar Musulmin duniya da su kauda kan su daga wannan aika aikan da suka danganta shi da ta’addanci.

Wannan dai yana zuwa ne kwana guda bayan Dan Siyasar Holland Geert Wilders da yayi fice wajen sukar addinin Islama ya nuna wasu zane zane har kala 10 da yake danganta shi da Manzan Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI