Faransa-Mali

Faransa za ta taimakawa kasar Mali inji Francois Hollande

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande Reuters/路透社

Shugaban Faransa Francois Hollande ya jaddada goyon bayan kasar ga al’ummar kasar Mali, tare da alkawali ci gaba da taimaka wa kasar domin ficewa daga matsaloli bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da kuma ‘yan tawayen kasar.

Talla

Wata sanarwa da fadar Elysees dake birnin Paris ta fitar jim kadan bayan tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Mali Ibrahim Boubakar Keita, Hollande ya ce Faransar za ta ci gaba da taimaka wa kasar a bangaren tattalin arziki da kuma siyasa domin samun nasarar wannan sulhu.

Faransa na daga cikin kasashen da suka taimaka  domin ceto kasar Mali daga  durkushewa bayan da yan tawayen arewacin kasar suka karbe ikon wasu yankunan kasar.

 

Gwamnatin  Mali ta bayana  matukar gamsuwar ta  a wanan tayi daga  Shugaban kasar Faransa Francois Hollande.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.